Artv News
Za a fara gasar kofin duniya kwana daya kafin ranar da aka tsara tun farko

Za a fara gasar kofin duniya ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, inda Qatar mai masaukin baki za ta kara da Ecuador.
Tun farko an tsara karawar rukunin farko ranar 21 da karfe 16:00 agogon GMT, kuma wasan Qatar shi ne na uku daga cikin wanda aka tsara yi.
An shirya da bude gasar da wasa tsakanin Senegal da Netherlands ranar Litinin 22 ga watan Nuwambar.
Daga baya Fifa ta karbi korafi daga hukumar kwallon kafa ta Kudancin Amurka da ake kira Conmebol, wadda ta ce bisa al'ada ana bikin bude gasa ko dai da mai rike da kofi ko kuma mai masaukin baki.
Za a zauna taro tsakanin hukumomin nahiyoyin duniya shida da shugaban Fifa, Gianni Infantino don fitar da matsaya.
Idan aka amince ba za a sauya ranar karawa tsakanin Senegal da Netherland ranar Litinin ba, illa wasan zai koma da karfe 16:00 agogon GMT.
Abinda zai sauya a ranar Litinin shi ne fafatawa uku za a yi maimakon hudun da aka tsara tun farko.
Za a buga wasan da aka shirya yi a rukuni na biyu tsakanin Ingila da Iran da karfe 13:00 GMT ranar 21 ga watan Nuwamba da kuma na Wales da Amurka da karfe 21:00 agogon GMT.