top of page
  • Writer's pictureArtv News

'Yar Najeriya Tobi Amusan ta kafa tahiri a gasar tseren duniya




'Yar Najeriya Tobi Amusan ta lashe kyautar zinariya a gasar mita 100 ta tseren mata ta Duniya da ake gudanarwa a Amurka.


'Yar wasan mai shekara 25 ta kafa tarihin ne a zagayen kusa da karshe inda ta kai layi cikin minti 12 da dakika 12.


A baya dai Ba'amurkiya Kendra Harrison ta kafa irin wannan tarihi a 2016 inda ta kai layi a minti 12 da dakika 20.


Amusan ta fi yin gudu a zagayen karshe ( ta yi minti 12 da dakika shida), amma ba a amince da nasararta ba saboda iska mai karfi da ke kara mata gudu.


Tobi ta zubar da hawaye don jin dadi a yayin da ake buga taken Najeriya a filin wasa na Hayward Field, Eugene da ke Jihar Oregon, saboda bajintar da ta yi wa kasarta.


'Yar kasar Jamaica Britany Anderson ta lashe kyautar azurfa yayin da 'yar kasar Puerto Rico wadda ita ce gwarzuwar gasar Olympic Jasmine Camacho-Quinn ta lashe kyautar tagulla.


Yayin da take bayani bayan ta samu nasara, Tobi ta ce: "Na yarda da kwazona amma ban taba tsammanin zan kafa tarihi a duniya ba."


BBC

6 views0 comments
bottom of page