Artv News
Yanzu-Yazu: Jam'iyyar APC ta Kano ta dakatar da shugaban jam'iyyar na Dambatta
Updated: May 30, 2022
Daga Kabiru Aluta

Uwar Jam'iyyar APC ta Jihar Kano karkashin Jagorancin Alhaji Abdullahi Abbas, ta dakatar da shugaban Jam'iyyar #APC na Karamar Hukumar Dambatta Alhaji Musa Sansan da Sakataren Jam'iyyar Abashe Umar na tsawon watanni shida don samun gudanar da bincike akan zarge-zarge da ake yi musu.
S

annan Jam'iyyar ta Jihar Kano ta na da Hon Muhammad Liman Danmasallaci (Party Legal Adviser) a matsayin sabon Shugaban Jam'iyyar na riko, sai Saidu Mukhtar (Assistant Secretary), a Matsayin Sakataren Jam'iyyar na riko.
Sakataren Jam'iyyar na Jiha Alhaji Ibrahim Zakari Sarina, shi ne ya mika takardar a gaban Shugaban Jam'iyyar na Jiha Alhaji Abdullahi Abbas da sakataren zartarwa na hukumar kula da jin dadin alhazai ta jahar Kano, Ambassada Muhammad Abba Danbatta