top of page
  • Writer's pictureArtv News

Yanzu-yanzu: Wasu 'yan ta'adda sun yi garkuwa da mahaifyrar AA Zaura


Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da, A.A Zaura. Da sanyin safiyar Litinin ne aka sace mahaifiyar ‘yar siyasar, Hajiya Laure Mai Kunu kafin al’ummar Musulmi su yi kiran Sallah. Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase, ya ce jami’an tsaro sun sanar da shi lamarin a hukumance. Ya ce an yi garkuwa da Hajiya Laure ne a gidanta da ke unguwar Rangaza a kauyen Zaura na karamar hukumar. Ko da yake rundunar ‘yan sandan Kano ba ta ce uffan ba kan lamarin.

206 views0 comments
bottom of page