top of page
  • Writer's pictureArtv News

Yanzu-yanzu: Jami'an hukumar EFCC sun kai sumame wajen gudanar da zaben fitar da gwani na PDP


Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a ranar Asabar din da ta gabata an gansu a filin wasa na Velodrome na filin wasa na Moshood Abiola, Abuja, na babban taron jam’iyyar PDP na kasa. Jami’an sun fito ne a cikin jajayen rigunansu da aka rubuta sunan hukumar a takaice Sun zagaya filin taron inda suka karbi bakuncin dubban wakilan jam'iyyar da ke jiran a fara zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben badi. Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ana tunanin jami'an yaki da cin hanci da rashawa sun kasance a cikin fage a matsayin hana masu son raba kudade don yin tasiri a sakamakon zaben. Babu wanda aka san jami’an sun kama shi a lokacin da aka gabatar da rahoton.

139 views0 comments
bottom of page