Artv News
'Yan wasan kwallon kafa sun zama bayin kudi - Laporta

Shugaban Kungiyar Barcelona Joan Laporta ya cacaki sabuwar kwangilar da ‘dan wasan gaba na kungiyar PSG Kylian Mbappe ya rattaba hannu wadda zata hana shi zuwa Real Madrid, inda yake cewa kwangilar ta rikita kasuwar ‘Yan wasa da kuma sabawa manufofin kungiyar kasashen Turai. Laporta yayi zargin cewar ana mayar da ‘Yan wasa bayin kudi, kamar yadda aka gani a kungiyar PSG wadda tayi iya bakin kokarin ta wajen hana Mbappe komawa Madrid kamar yadda ya nuna sha’awar sa a baya. Kamar yadda gidan rediyon RFI ya rawaito, Shugaban kungiyar ya bayyana cewar duk da yake zaman Mbappe a kungiyar PSG shine farin cikin kungiyar Barcelona, ganin cewar ba zai koma Madrid har ya zama musu barazana ba, amma yana da kyau ayi magana akan ci gaban wasan gaba daya.
Dangane da batun ko Neymer na iya komawa Barcelona kuwa, sai Laporta yace ‘dan wasan na da kwangilar da zata kai shi shekaru 4 zuwa 5 masu zuwa, yayin da ya kara da cewar ‘yan wasan da suka koma kungiya irin ta PSG sun tafi akin bauta ne domin samun kudi.
Hukumar gudanarwar La Liga tayi barazanar maka PSG a kotun Turai bayan da Mbappe ya sanar da cewar zai ci gaba da zama a kungiyar.