top of page
  • Writer's pictureArtv News

’Yan Sanda Sun Kama Dan Takarar Sanatan NNPP A Maiduguri


’Yan sanda sun cafke dan takarar Sanatan Borno ta Tsakiya a majalisar Dattijai na jam’iyyar NNPP, Hon Attom Muhammad Maigira, sannan an kulle ofishin jam’iyyar da ke Maiduguri.


Hukumar Raya Birane ta Jihar ta Borno ce dai ta rufe ofishin jam’iyyar ranar Alhamis.


Dan takarar Gwamnan jihar a jam’iyyar ta NNPP, Dokta Umaru Alkali ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a Maiduguri.


Ya kuma ce an kama dan takarar Sanatan nasu ne bayan ya ki amsa gayyatar da ’yan sandan suka yi masa, kuma yanzu yana tsare a hannunsu.


Umaru Alkali ya ce an kuma jibge tarin jami’an tsaro a sakatariyar jam’iyyar da ke kan titin Abbaganaram da Gidan Madara tsakanin Laraba zuwa Alhamis don hana ’yan jam’iyyar shiga cikinta.


Da majiyarmu ta ziyarci sakatariyar da misalin karfe 11:30 na safe, ya iske ’yan sanda da jami’an tsaron rundunar CJTF da motocin sintiri a wajen.


Muna tafe da karin bayani…

113 views0 comments
bottom of page