Artv News
Yan majalisar Amurka sun yi mun kama-karya - Trump

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi Allah wadai da binciken da majalisar dokokin kasar ta gudanar kan tarzomar da magoya bayansa suka yi a bara yana mai bayyana hakan a matsayin kama karya. A cikin wata sanarwa mai shafi 12 da ya fitar, Trump ya ce maimakon mayar da hankali kan manyan matsalolin kasar, kwamitin da za a ce na bisa tafarkin dimokradiyya ya kasance dan amshin shata, ta hanyar kawar da hankalin jama'ar Amurka daga matsanancin radadin da suke fuskanta zuwa binciken abinda bashi da amfani a ganinsa.
Kwamitin dai na gudanar da zaman sauraron korafe-korafe har guda shida da nufin gano dalilin da ya sa aka sami wannan tarzoma daga magoya bayan Donald Trump din a bara. Sai dai tuni aka yi wasti da guda daga cikin kararraki 62 da kwamitin yakin neman zaben
Trump ya shigar, karkashin amincewar akasarin alkalan da jam'iyyar Republican ta nada. Shugaban kwamitin Bennie Thompson a jawabin bude taron tattaunawar da ya gabatar, ya ce duk da cewa Trump ya san cewa ya fadi a zaben, amma ya kekashe kasa ya ki amaincewa, maimakon hakan sai ya fara kaiwa bangaren dimokradiyya hari.