top of page
  • Writer's pictureArtv News

‘Yan Majalisa sun soki yawan 'yan tawagar da Buhari ya kai Amurka


Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun soki tawagar kusan mutum 100 da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta zuwa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.


'Yan majalisar da ke sukar tawagar, sun ce bai kamata a haɗa dandazon jama’a kusan mutum dari ba a wannan lokaci da Najeriya take fama da matsin tattalin arziki.


A taron da ke zamar wa Buharin na karshe a matsayin shugaban kasa.

Shugaban ya yi jawabinsa na ban-kwana a wajen babban taron.

Sai dai ‘yan majalisar irin su Sanata Muhammad Sani Musa, na Majalisar Dattawa, ya ce wannan taro ne da ake yi a kowacce shekara kuma kowa ya ga irin ayarin da yake dauka wajen tafiya irin wadannan tarukan tun hawansa mulki.


'Na ji kunya'


Sanatan ya ce zance na gaskiya akwai rashin kyautawa da adalci, musamman a bangaren mashawarta ko mukarraban shugaban kasar da yake cewa ba sa fada masa gaskiya ko kyautata masa.


Ya ce: ''Da ake nuna tawagar a talabijin har kunya na ji, saboda ana kuka a kasa cewa babu kudi, har ana tunanin ciyo bashi domin cike gibin kasafin kudi, to ina dalilin wannan tafiya?'', a cewar sanatan.


Sanatan ya kuma ce duk waɗannan tawaga karkashin gwamnati dole a biya musu kudin tikiti da dakin kwana da abinci da kuma kudaden alawus.

‘Ake sara ana duba bakin gatari’


Sanatan ya ce a bara an yi irin wannan tafiya, kuma galibin ‘yan tawagar sun halarta, don haka menene dalilin sake maimaita tafiyar da irin wannan tawaga.


Ya ce idan mutum na da abin yi ko wadanda taron ya shafa kai-tsaye, misali idan fannin ilimi ake magana sai a tafi da masu ruwa da tsaki a wannan fanni, ba wai a kwashi dandazon jama’a ba.


Dan majalisar ya ce duk da cewa ana cewa irin wannan tawaga ta je ne domin tattaunawar bayan fagge kan batun zuba jari.


Ya ce ai babu wanda zai je farauta a wannan hali da Najeriya ke ciki.


Ya kara bayani da cewa: ‘'Idan aka inganta Najeriya ba a bukatar a tafi neman masu zuba jari, za su zo da kansu.’'


Sannan dan majalisar ya ce ya yi imanin cewa shugaban kasar bai san adadin mutanen da suka tafi Amurka da sunanshi ba.


Yana mai zargin cewa, ''Duk mukarrabansa ke shirya irin wadanan abubuwa.''


Dan majalisar na cewa akwai muhimman abubuwa na gida da tsari da ake bukatar a gyara, wadanda su ya kamata ake bai wa fifiko a wannan lokaci.


Sannan ya jaddada muhimmancin tausaya wa kasa da rage barnatar da kudaden gwamnati in dai an shirya gyara domin samar da ci-gaba.

(BBC HAUSA)

13 views0 comments
bottom of page