Maryam Yahaya: Tauraruwar fina-finan Kannywood ta ce maleriya da taifod ne ke damunta
Updated: Aug 3, 2021
Tauraruwar fina-finan Kannywood Maryam Yahaya ta bayyana cewa tana fama da cutar maleriya da taifod, shi ya sa aka ji ta shiru ba ta fitowa a fina-finai.

Ta bayyana haka ne a wata hira da BBC domin yin watsi da rahotannin da ke cewa tana fama da cutar da ta danganci jifan aljanu.
Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, wanda ya yi tafiyayya zuwa gidan su tauraruwar, ya ce ta yi matukar ramewa.
Sai dai a cewarta: "Na yi taifod da maleriya ne, ina kan yi. Amma yanzu jiki Alhamdulillahi, na samu lafiya."
Da take amsa tambaya kan raɗe-raɗin da ke cewa an yi mata asiri ko jifa, tauraruwar ta ce "gaskiya ni ba jifa ba ne ya dame ni don ban ma san shi ba."
Ba a hada aure da yin fim - Maryam Yahya
Zainab Booth: 'Yar wasan kwaikwayo kuma mahaifiyar Maryam Booth ta rasu
Ta ce ta kwashe fiye da wata ɗaya tana fama da rashin lafiya, tana mai cewa yanzu tana samun sauki sosai, "sai dai rashin ƙwari kuma dama sai a hankali ƙwari yake zuwa."