top of page
  • Writer's pictureArtv News

’Yan Kaduna Za Su Yi Kewar El-Rufa’i Idan Ya Bar Mulki – Uba Sani


Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, ya ce ’yan jihar za su yi kewar mulkin Gwamna mai ci, Nasiru El-Rufa’i idan ya bar mulki a 2023.


Wa’adin mulkin El-Rufa’i zai zo karshe ne a a karshen watan Mayun 2023, lokacin da zai kammala zango na biyu na mulkinsa na shekara takwas.


Dan takarar ya bayyana Gwamna mai ci a matsayin mai gaskiya kuma wanda ba ya shayin yin abin da ya dace da kuma ya shimfida wa jihar ayyukan alheri.

Uba Sani, wanda kuma shi ne Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, ya ce kodayake ba za a rasa kura-kurai nan da can ba a matsayinsa na dan Adam, Gwamnan ya yi matukar kawo wa jihar ci gaba.


Ya yi wadannan kalaman ne a yayin wata tattaunawa da ’yan jarida wacce Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya wa dukkan ’yan takarar Gwamnan Jihar.


Ya ce, “El-Rufa’i mutum ne mai gaskiya wanda ba za a zarge shi da rashawa ba. Ya yi Ministan Abuja sama da shekara 15 da suka gabata, amma har yanzu suna can suna kewarsa. A Kaduna ma za a yi kewarsa idan ya bar mulki a 2023,” inji shi.


Uba Sani ya ce Gwamnan ya taka rawar gani wajen raya birane da bunkasa lafiya da ilimi da kuma sauran fannonin bunkasa rayuwar dan Adam.


Da ya juya bangaren tsaro kuwa, dan takarar ya ce kirkiro ’yan sanda jihohi ce babbar hanyar magance matsalar ’yan bindiga a Najeriya, musamman ma a jihar Kaduna.


Ya ce a matsayinsa na Sanata, ya yi matukar kokarin ganin an yi gayaran fuska ga kudurin da zai ba ’yan sa-kai damar daukar makamai don kare yankunansu.

(AMINIYA)

0 views0 comments
bottom of page