Artv News
Ya zama wajibi mu dawo da tsaro a yanki Tera - Bazoum

Shugaban Jamhuriar Nijar, Bazoum Mohamed ya ziyarci yankin Tera dake kusurwar kasashe uku masu fama da haren-haren yan ta’adda, Mali,Burkina da Nijar. Akalla yan gudun hijira 13.500 ne suka samun mafaka a yankin. Shugaban na Nijar Bazoum Mohamed yayi amfani da wannan dama tare da shigar da bukatar ganin an samu hadin kai tsakanin kabilu dake zaune a wannan wuri,hakan zai kuma taimaka don murkushe barrazanar yan ta’adda dake kokarin wargaza daddadiyar zaman lafiya na wannan yanki.
Yankin Tera dake kusurwar kasashen Burkina Faso,Mali da Nijar ya kasance wani yanki da hukumomi ke iya kokarin ganin sun murkushe duk wani al’amari da ya shafi ta’addanci.
Shugaban na Nijar ya yi bita gameda da irin kalubale da Nijar ke fuskanta domin tabbatar da tsaro a yankin na Tera.
Shugababn na Nijar ya kira hukumomin kasashen Burkina Faso da Mali na ganin sun bayar da goyan bayan da ya dace a wannan kokari da Nijar ke yi na kawo karshen bata gari da ke amfani da addinin musulunci wajen aikata miyagun laifuka,musamman ta’addanci.
Kauyen Diagourou ya zama kufai ,garin da rashin tsaro ya tabbata kamar dai yada magajin garin Hama Boukari ya tabbatar mani. Babu wata makaranta dake aiki a wadannan yankunan,babu wani jami’in gwamnati dake iya zuwa kauyen na Diagourou, alkaluman da muke da su dagatai 23 daga cikin 43 da muke da suka bar yankin.
Akalla dakarun kasdar ta Nijar 3000 ke cikin shirin ko ta kwana a wannan yaki dare da rana da mayakan jihadi kamar yadda RFI ta rawaito