Artv News
William Ruto ya lashe zaben shugabancin kasar Kenya

Mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto ya lashe zaben shugabancin kasar, inda ya kayar da abokin burmin sa Raila Odinga wanda ke samun goyon bayan shugaban kasar Uhuru Kenyatta.
Shugaban hukumar zaben kasar Kenya a ranar Litinin ya ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, duk da cewa wasu kwamishinonin sun ki amincewa da sakamakon zaben.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Wafula Chebukati ya ce Ruto ya lashe zabe da kusan kuri'u miliyan 7.18 (kashi 50.49) yayin da abokin hamayyarsa Raila Odinga ya samu kuri'u miliyan 6.94 (kashi 48.85).