top of page
  • Artv News

West Ham ta amince da farashin sayen Onana kan fam miliyan 35.5 daga Lille


West Ham ta amince da farashin da aka yi wa Amadou Onana kan fam miliyan 33.5 har da karin tsarabe-tsarabe daga Lille.


West Ham na kokarin bunkasa 'yan wasanta karkashin David Moyes a shirin da take na tunkarar kakar bana da za a fara cikin Agustan nan.


Har yanzu ba a kammala cinikin dan kwallon mai shekara 20 ba, domin dan wasan bai kai ga cimma matsaya ba kawo yanzu.


Haka kuma West Ham na sha'awar daukar dan wasan Burnley, mai shekara 25, Maxwel Cornet, wanda ya ci kwallo tara a wasa 25 a kakar da ta wuce.


Onana wanda aka haifa a Dakar - ya fara tamaula daga tawagar matasan Belgium zuwa manyanta da buga Nations League a karawar da Netherlands ta yi nasarar 4-1 a watan Yuni.


Onana ya taka leda a Hamburg kafin fara kakar 2020/21 a matasan kungiyar daga baya ya koma cikin kwararrun 'yan wasanta da murza leda.


Ya koma Lille a Agustan 2021 da buga mata wasa 31 a Ligue 1 a kakar da ta wuce da yi mata dukkan wasannin Champions League a bara.


West Ham na fatan daukar Onana na biyar a bana, bayan mai tsaron raga Alphonse Areola da mai buga tsakiya Flynn Downes da mai tsaron baya Nayef Aguerd da mai cin kwallaye, Gianluca Scamacca.

4 views0 comments
bottom of page