top of page

Attahiru Jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaɓen APC da PDP

Updated: Aug 3, 2021

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya, Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya yi kira ga 'yan ƙasar su dawo daga rakiyar manyan jam'iyyu na APC da PDP, saboda yadda suka kasa taɓuka wani abun arziƙi a tsawon shekara 20 da suka shafe suna mulkiYayin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Jega ya ce muguwar rawar da jam'iyyun biyu suka taka a tsawon waɗannan shekaru ta nuna ƙarara cewa babu buƙatar a sake yin amanna da su a kan cewa za ta sauya zani idan aka sake ba su wata dama a nan gaba.

Ya ce: "APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba.

"Idan ka dubi yaƙi da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa ɓarayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaba sun koma APC, kuma shiru kake ji.

Jega ya ce ''shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya.

6 views0 comments
bottom of page