top of page
  • Writer's pictureArtv News

UMAR ABDULLAHI GANDUJE YA ZAMA DAN TAKARAR MAJALISAR TARAYYA A YANKIN D/TOFA,R/GADO DA TOFA




A daren wannan rana ta Alhamis, 26 ga watan mayu 2022, Dr. Junaidu Yakubu me neman takarar Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa ya janyewa Engr. Umar Abdullahi Ganduje Takararsa a zaben fitar da gwani na Jamiyyar APC da za'ayi a gobe insha Allah.


Anyi wannan zaman ne a bisa Shugabancin Sanatan Kano ta Arewa Barau I. Jibrin da Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi.


Taron ya samu Halartar Shugabannin Kananan Hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, Kwamishinonin wannan yanki da Dattijan Jamiyyar APC na wannan yankin.

358 views0 comments
bottom of page