Artv News
Ukraine ta janye dakarunta daga Donbas bayan tsanantar hare-haren Rasha

Mahukuntan Ukraine sun umarci dakarun sojin kasar su janye daga sassan Severodonetsk da ke yankin Donbas, bayan shafe makwanni suna gwabza yaki da Sojin Rasha da ke kokarin kwace iko da babban birnin na gabashin kasar. RFI ta rawaito cewa, janyewar dakarun na Ukraine daga Severedonetsk na zuwa ne bayan karfafa hare-haren Sojin Rasha a yankin na Donbas a ci gaba da kokarin kwace iko da yankin mafi girma a gabashin Ukraine dai dai lokacin da kungiyar EU ta baiwa kasar damar zama mambarta.
Tun bayan faro mamayar ta Rasha ga Ukraine a karshen watan Fabarairu, kasar ta tsohuwar tarayyar Soviet ta mika bukatar shiga EU don zame mata kariya daga barazanar Rasha said ai duk da matakin amincewar kungiyar hakan bai hana makwabciyartata ci gaba da mamaye manya kuma muhimman yankunan Kiev ba.
Bayan fatattakar sojinta a Kiev, Rasha ta karkata ilahirin karfinta zuwa yankin na Donbas da ke gabashin Ukraine inda ta ci gaba da kwace kananun garuruwa da birane gabanin kai wa ga Severedonetsk da dakarun na Moscow ke gab da kwacewa.
Gwamnan Lugansk yankin da ya kunshi har Severedonekts Sergiy Gaiday ya ce duk da asarar rayukan da ake musu dakarun Rasha na ci gaba da kutsawa sassan yankin wanda ke nuna dole su janye dakarunsu.
A cewar gwamnan dakarun Rasha sun lalata kashi 90 na yankin kuma zuwa yanzu yankunan masana’antu ne kadai ke karkashin ikon Ukraine.