top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ukraine na neman karin makaman yaki


Kasar Ukraine ta sake yin kira ga kasashen duniya su samar mata da karin makaman yaki domin tunkarar mamayar Rasha.


Shugaba Volodomyr Zelensky ya shaida wa taron kungiyar NATO a ranar Asabar cewa: “Muna bukatar mu karya lagwon makaman Rasha. Muna bukatar karin makamai na zamani.”


Ya ce, idan Ukraine ba ta samu makaman da take bukata ba, to shugabannin NATO za su fuskanci yaki a nan gaba.


Kasashe sama da 30 ne suka bai wa kasar Ukraine dimbin kayan yaki, sai dai ana tafiyar hawainiya game da manyan makamai, kuma a wasu yankunan sojojin Ukraine ba su da makamai.


Aminiya ta rawaito Kwararun sojoji na cewa, samun nasara a fagen daga na bukatar manyan makamai da horo da kayan gyara da sauran tallafi.


A yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da luguden wuta a yankunan Ukraine, manazarta sun ce, Ukraine tana matukar bukatar ingantattun makamai da harsasai don rike manyan yankunanta.


Zuwa yanzu, ana tunanin cewa an tura wa kasar makaman roka 10 masu cin dogon zango ko kuma suna kan hanya daga Amurka da Birtaniya da Jamus.


Ukraine ta ce, ana bukatar wasu da dama don dakile dannawar sojojin Rasha. kasashen Amurka da Jamus ne suka fi ba Ukraine tallafi a yakin.


Birtaniya ita ce ta biyu yayin da Poland ita ce ta uku a jerin kasashen da ke kashe wa Ukraine makudan kudade.


Dangane da kudaden da aka kashe, maimakon alkawuran bayar da kudi da kasashe suka yi, Fadar White House ta ce, Amurka ta bayar da tallafin Dala biliyan 6.3 a matsayin taimakon tsaro ga Ukraine tun lokacin da Shugaba Joe Biden ya hau karagar mulki a watan Janairun bara.


Birtaniya kuma ta samar da Dala biliyan 1.6, kuma ta yi alkawarin bayar da karin Dala biliyan 1.2 tun farkon yakin. Shugaba Zelensky ya nemi karin kudade, kuma ya ce kudaden da kasar ke kashewa kan tsaro a kowane wata ya kai kusan Dala biliyan 5.

7 views0 comments
bottom of page