Artv News
Tinubu Ya Zama Dan Takarar Shugaban Kasar APC

Tsohon Gwaman Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya zama dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a zaben 2023.
Tinubu ya lashe zaben ne bayan ya kere sauran abokan karawarsa da mafi yawan kuri’un da daliget sama da 2,00o suka jefa a zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a ranar Laraba.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton, Tinubu na da kuri’a sama 1,000 a yayin da mai bi mishi, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ke bi mishi da kuri’a 316.
Tun kafin gudanar da zaben, mutum bakwai daga cikin mutum 23 da ke neman tikitin a karkashin inuwar jam’yyar, suka janye wa Tinubu.
Suran ’yan takarar da kuri’un da suka samu sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima wanda ya samu kuri’a hudu.
Kuri’un da sauran ’yan takarar suka samu zuwa yanzu su ne:
Chubuike Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Sufuri – 316
Farfesa Yemi Osinbajo, Matamakin Shugaban Kasa, – 235
Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa – 152
Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi – 47
David Umahi, Gwamnan Jihar Ebonyi – 38
Ben Ayade, Gwamnan Jiyar Kuro Riba – 37
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima – 4
Chukwuemeka Nwajiuba, tsohom Minista a Ma’aikatar Ilimi – 1
Dokta Christopher Onu – 1
Sanara Rochas Okorocha, tsohon Gwamman Jihar Imo – 0
Fasto Tunde Bakare, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa – 0
Tien Jack-Rich – 0
Abasi Ikoli – 0