top of page
  • Writer's pictureArtv News

Tinubu ya ce bai isa ya raina Buhariba


Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar, Bola Tinubu ya ce raina Shugaba Muhammadu Buhari baya daga cikin hayallarsa.


Kalaman nasa na zuwa ne biyo bayan tayar da kura da kalaman da ya yi a wata ganawa da ya yi da daliget din APC a jihar Ogun suka yi.


A wajen ganawar ta jiya Alhamis, Tinubu ya ce ba don shi ba da Buhari ya fadi zaben 2015.

Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, Tinubu ya ce bai fadi hakan da nufin yi wa Buhari rashin ladabi ba kamar yadda BBC Hausa ta rawaito



Ya ce da yawa ko dai ba su fahimci kalamansa ba ko kuma sun yi musu wata fassara ta daban.

Tinubu ya ce "Ina alfahari da kaina kan rawar da na taka a nasarar da APC ta sha yi. Amma tabbas Shugaba Buhari shi ne babban jagoran nasarar. "Sau biyu ana zabarsa a matsayin shugaban kasa.


Ya jagoranci kasar nan tsawon shekara bakwai, babu mai karyata hakan.

Ban isa na raina abin da ya yi ba ko raina matsayinsa a APC da Najeriya ba," in ji Tinubu.

11 views0 comments
bottom of page