Artv News
Tinubu ne ya fi dacewa da mulkin Najeriya, In ji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne mutumin da ya fi dacewa ya gajeshi a takarar shugabanci a Najeriya.
Tinubu ya samu tikitin takara a APC a zaɓen fitar da gwani da aka kammala jiya Laraba a Abuja.
Shugaban a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Malam Garba Shehu, na cewa yana tare da Tinubu kuma zai mara ma sa baya wajen cimma nasara a zaɓen 2023.
Ya kuma ce Tinubu shi ne mutumin da zai kare da inganta tsarin dimukuradiya da suka gina kasar a kai.
Shugaban ya kuma bukaci 'ya'yan jam'iyyar su hada kai wajen cimma nasara a zaɓen 2023.
Article share tools