top of page

Darajar Bitcoin ta faɗi a Duniya

Updated: Aug 4, 2021

Babban birnin kasar China (Beijing) ta haramta wa bankuna da kamfanoni biyan kudade daga gudanar da ayyukan da suka shafi mu’amala da kudin na Bitcoin.




Babban birnin kasar China (Beijing) ta haramta wa bankuna da kamfanoni biyan kudade daga gudanar da ayyukan da suka shafi mu’amala da kudin na Bitcoin.

Ta kuma gargadi masu zuba jari a kan batun huddar cinikayyar ta kudin na intanet a ranar Talata.

Ya biyo bayan faduwar darajar Bitcoin din da fiye da kashi goma bisa dari (10%) a makon jiya bayan da kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki Tesla ya ce ba zai cigaba da amincewa da karbar kudin na intanet ba.

A ranar Laraba ne, Bitcoin din ya sake farfadowa, duk da cewa har yanzu yana kasa – kashi goma da kadan bisa dari (10.4%) a dala dubu talatin da takwas da dari da talatin da daya ($38,131).


Ta wani gefen kuma, sauran kudaden intanet kamar su Ether, da Dogecoin sun yi asarar kashi ashirin da biyu bisa dari (22%) da kashi ashirin da hudu bisa dari (24%) daban-daban.

A karon farko cikin watanni uku a ranar Laraba, farashin Bitcoin ya fadi kasa da dala dubu talatin da hudu ($34,000) kwatankwacin fan ashirin da hudu da talatin (£24,030), bayan da kasar China da kafa sabuwar dokar haramci kan amfani da kudin na intanet.



7 views0 comments
bottom of page