Artv News
Ten Hag ya caccaki Ronaldo da ya bar fili tun kan tashin wasan sada zumunta

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce ''ba zai amince'' da dabi'ar wasu 'yan wasa har da Cristiano Ronaldo da suka bar Old Trafford tun kan tashi daga wasan sada zumunta ranar Lahadi.
Manchester United ta shi wasan sada zumunta da Rayo Vallecano 1-1 a karshen mako na karshe da ta yi don shirin tunkarar kakar bana.
Bayan da kungiyoyi suka je hutu ne aka canja Ronaldo, wanda karon farko da ya yi wa United tamaula kenan a bana.
An dauki hoton Ronaldo tare da Diogo Dalot da wasu sauran 'yan wasan kungiyar na fita daga Old Trafford saura minti 10 a tashi daga fafatawar.
''Mu kungiya ce madaurinmu daya da ke nufin mu kasance tare har sai bayan wasa,'' kamar yadda Ten Hag ya sanar da Viaplay.
''Ba zan taba amincewa da haka ba daga wadanda suka aika wannan dabi'ar.''
Ronaldo mai shekara 37, wanda ya koma United a bara na son barin Old Trafford domin buga Champions League a bana.
United wadda ta yi ta shi a Premier League a bara za ta buga Europa ;eague a kakar nan.
Kyaftin din tawagar Portugal bai je atisayen da United ta yi a Thailand da Australia ba, saboda wasu dalilai da suka shafi iyalinsa.
A can baya ne Ten Hag ya sanar da cewar Ronaldo "bana sayarwa bane" yana cikin 'yan wasan da zai yi amfani da su a bana.
Sabbin 'yan wasan da United ta dauka a bana Christian Eriksen da Lisandro Martinez duk sun buga mata wasan sada zumunta da Vallecano ranar Lahadin.
United za ta fara kakar bana 2022-23 a gasar Premier League da karbar bakuncin Brighton ranar Lahadi 7 ga watan Agusta.
(BBC Hausa)