top of page
  • Artv News

Tawagar Sojin Faransa ta karshe ta kammala ficewa daga Mali bayan yakin shekaru 9


Ma’aikatar tsaron Faransa ta tabbatar da ficewar rukunin karshe na Sojinta da ke yaki a Mali bayan shafe shekaru 9 suna fatattakar mayakan kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi, ficewar da ke zuwa bayan tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu tun bayan juyin mulkin Soji a bara waccan.

Sanarwar da shalkwatar tsaron Faransa ta fitar ta ce da misalin karfe 11 na dare ne tawagar karshe ta motocin da ke dauke da Sojin suka ratsa iyakar Malin da Nijar wanda ke kawo karshen ci gaba da kasancewarsu a cikin Bamako.

Biyo rikicin da ya tilasta ficewar Sojin na Barkhane Faransa ta ce rundunar ta sake gina kanta a kasashen makwabta cikin kasa da watannin 6 da taimakon sojojin kawancen da ke taimakawa a yaki da ta’addancin.

Sanarwar ta ce Faransa za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin tsaro a yankin Sahel da Tafkin Chadi da kuma mashigin ruwan Guinea don tabbatar da zaman lafiyar nahiyar Afrika.
6 views0 comments
bottom of page