top of page
  • Artv News

Takarar Sanata: Kotu Ta Umarci INEC Ta Tabbatar Da Akpabio


Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta dawo da sunan Ministan Neja Delta, Godwill Akpabio, a matsayin dan takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, na Jam’iyyar APC a zaben 2023.


Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin ne ranar Alhamis bayan hukumar ta cire sunan Akpabio — wanda ya nemi takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC kafin daga baya ya janye — a matsayin dan takarar sanata.


A baya dai jam’iyyar APC ta mika wa INEC sunan Akpabio a matsayin dan takarar Sanatan Akwai Ibom ta Arewa maso Yamma.


Ta kuma mika wa sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan — wanda aka kayar a zaben dan takarar shugaban kasa a APC — a matsayin dan takarar Yobe ta Arewa.


Kazalika jam’iyyar ta gabatar da Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi, wanda ya yi zawarcin kujerar shugaban kasa, a matsayin dan takarar Sanatan Ebonyi ta Kudu.


Sai dai kuma a jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta fitar babu sunan ko daya daga cikin su hudun.

0 views0 comments
bottom of page