top of page
  • Writer's pictureArtv News

Sojojin Najeriya sun kwace tarin makamai daga 'yan bindiga


Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kwato makamai 706 daga hannun 'Yan bindiga da bata gari a ayyukan da take gudanarwa a Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi.

Kwamandan rundunar Hadarin Daji dake yaki da bata gari da ake kira Manjo Janar Uwem Bassey ya gabatar da wannan adadi lokacin da yake mika makaman ga Hukumar yaki da yaduwar kanana da matsakaitan makamai shiyar Sokoto.

RFI ta rawaito cewa, Janar Bassey wanda sh ine Babban Kwamandan rundunan soji ta 8 dake Sokoto yace dakarun sa sunyi nasarar kakkabe makaman daga hannun Yan ta’adda ne a samamen da suka kaddamar daban daban a jihohin dake Yankin Arewa ta Yamma.

Alkaluman da Janar Bassey ya gabatar sun nuna cewar akwai bindiga kirar AK-47 203 da wasu masu sarrafa kansu guda 4 da ake kira a gida da samfurin G3 guda 7 da GPMG guda da kuma kananan masu sarrafa kan su guda 3.

Kwamandan ya yabawa jama’ar yankin saboda rawar da suke takawa wajen bada bayanai masu muhimmanci ga jami’an tsaro wadanda suka taimaka wajen samun wannan nasara.

Yayin da yake karbar bindigogin, Jami’in dake kula da shiyar Sokoto na Hukumar yaki da yaduwar makaman, AVM Haruna mohammed ya jinjinawa dakarun saboda gagarumar rawar da suka taka, inda ya bayyana kwarin gwuiwar samun fiye da haka nan gaba.

30 views0 comments
bottom of page