top of page
  • Writer's pictureArtv News

Shugaba Buhari ya nemi 'yan takarar shugaban kasa su sasanta kansu


Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar APC su sasanta a tsakaninsu don amincewa da mutum guda ya wakilci jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe.


Shugaban ya ba su shawarar ne yayin wata ganawa da ya yi da su da daren ranar Asabar a fadarsa da ke Abuja.


Dukkan masu neman takarar sun halarci wannan ganawa, ciki har da jagoran jam'iyyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda a baya-bayan nan ya furta wasu kalamai kan shugaban, da suka tayar da ƙura.



Sai dai yayin wata zantawa da BBC Hausa, mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya musanta wasu rahotanni da wasu kafafen watsa labaran Najeriyar ke watsawa, da ke cewa shugaban ya goyi bayan kai mulki kudu.



''Wannan magana ba ta taso ba, abun da kawai ya ce shine su tattauna su fitar da mutum guda a cikinsu, kuma ya nuna cewa a matsayinsa na shugaba a shirye ya ke ya ba da jagoranci don ganin cewa hakan ta tabbata'' in ji shi.


Gabanin ganawar dai an yi ta tunanin cewa a lokacin ne shugaba Buhari zai fadi wanda yake goyawa baya gabanin zaɓen fitar da gwani na APC da ake sa ran gudanarwa cikin makon da za a shiga.


To amma kakakin shugaban Malam Garba Shehu bai kore yiwuwar hakan ba, inda ya ce idan shugaban ya yi shawara da waɗanda suka kamata to akwai yiwuwar a yi irin abun da aka yi lokacin zaben shugaban APC da aka yi baya bayan nan, inda Buharin ya goyi bayan Abdullahi Adamu a ƙurarren lokaci.


Kafin ganawar da shuga Buhari ya yi da ƴan takarar dai wata sanarwar hadin guiwa da wasu gwamnonin APC 11 na arewa suka fitar, ta bukaci dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar su janye don miƙa wa kudu mulki.


13 views0 comments
bottom of page