top of page
  • Writer's pictureArtv News

Sarki Salman ya gana da Shugaban Amurka a Jedda


Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul-aziz tare da Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman sun gana da shugaban Amurka Joe Biden a birnin Jidda.


A cewar Jaridar Aminiya, Kamfanin Dillacin Labaran kasar na SPA ya ruwaito cewa, shugaban na Amurka tare da tawagarsa sun samu kyakkyawar tarba a lokacin ziyarar tasu zuwa fadar sarkin na Saudiyya.



Yayin ganawar shugabannin biyu a ranar Juma’a, sun tabo batun tarihin alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma bijiro da hanyoyin kara inganta dangatakar da ke tsakaninsu.


Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai babban mai bai wa Sarkin shawara kan harkokin tsaro Dokta Musaed bin Mohammed Al-Aiban da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da Mai ba da shawara kan Harkokin Tsaro, Jake Sullivan.

15 views0 comments
bottom of page