top of page
  • Writer's pictureArtv News

Sama da Alhazai 940 za su rasa yin aikin Hajjin bana daga jihar Kano sakamakon rashin jirgi


Da yake zantawa da manema labarai a safiyar yau alhamis Sakataren zartarwa na hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, , Muhammad Abba Danbatta, ya ce lamarin ya yi matukar sanya shi bakin ciki ganin yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta gaza cika alkawarin taimakawa wajen kwashe ragowar maniyyatan na Kano


Danbatta ya ce a yau, jirgin AZMAN mai daukar fasinjoji 400 zai tashi daga Kano dauke da maniyyata 250 kacal, inda ya bar sama da alhazai 940 tare da jami’an jihar.


Hukumar kula da aikin Haji ta kasa (NAHCON) ta yi alkawarin tura kamfanin jirgin Flynas tun kwanaki biyu da suka gabata don ceto lamarin amma har yanzu ba hakan ba ta tabbata ba

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya kara da Kamfanin jirgin saman AZMAN ya yi jigilar maniyyata sau shida da mahajjata 1,175 saboda suna da kananan jiragen da ba su da karfin daukar alhazai masu yawa.

Danbatta ya ci gaba da cewa wannan ne ya sa muka koka kafin a fara aikin Hajji ganin cewa muna da mafi yawan alhazai, cewa mun gwammace a dauke mu da jirgin Max Air.


Sakataren zartarwar ya kara da cewa ya kasance a Abuja sama da sau 10 a hedikwatar NAHCON akan wannan batu, yace ya rubutawa hukumar wasiku sama da 11 don kada a shiga cikin wannan hali kuma gwamnan ta rubuta musu har sau 3 amma abin da suka kokarin karewa ya kusa faruwa yanzu


362 views0 comments
bottom of page