top of page
  • Writer's pictureArtv News

Sadio Mane: Bayern Munich za ta sayi dan wasan Liverpool a kan £35m


Liverpool ta amince ta sayar wa Bayern Munich dan wasanta Sadio Mane a kan euro 41m (£35.1m).


Munich za ta biya euro 32m (£27.4m) kan dan wasan tare da karin euro 6m na tsarabe-tsarabe bisa shigarsa wasanni da kuma karin euro 3m idan ya yi kwazo.


Sau biyu Liverpool tana yin watsi da tayin da Bayern ta yi mata kafin ta amince ta sayar da dan wasan mai shekara 30, wanda kwantaraginsa da Reds za ta kare a bazara.


Liverpool ta saye shi daga Southampton a shekarar 2016 a kan £31m da karin £2.5m na tsarabe-tsarabe.


Tun daga wancan lokacin, Mane ya zura kwallaye 90 na Gasar Firimiya a wasannin da ya yi wa kungiyar sannan ya kammala kakar wasan da ta wuce da cin kwallaye 23 a gasa daban-daban da ya yi wa Liverpool.


Labarin barinsa Liverpool ya fito ne ranar Talata lokacin da kungiyar ta bayyana sayen dan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez daga Benfica a kan £64m.


Mane yana cikin 'yan wasan da suka bayar da gudunmawa sosai wajen nasarar Liverpool a shekarun baya bayan nan, tare da 'yan wasan gaba Mohamed Salah da Roberto Firmino, wadanda dukkansu suke da shekara 30 a duniya.


'Yan wasan uku sun taimaka wa kungiyar wajen daukar kofin Zakarun Turai a 2019 da kuma kofin Gasar Firimiya ta Ingila, wadda suka shekara 30 ba su dauka ba.


Wannan shekarar ta kasance mai muhimmanci ga Mane, domin kuwa ya lashe gasar cin Kofin Afirka da kasarsa ta Senegal sannan ya taimaka wa Liverpool wajen daukar kofin Carabao da FA sannan suka zo na biyu a Premier League da Champions League.


Ana sa ran Mane zai maye gurbin Robert Lewandowski a Bayern, yayin da dan kasar ta Poland yake shirin barin kungiyar kuma ana rade radin zai tafi Barcelona.

8 views0 comments
bottom of page