top of page
  • Writer's pictureArtv News

Rushewar gini a Kano : Gwamna Ganduje ya mayar da filin wajen ajiyar ababan hawa


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya soke izinin ginin wurin da wani bene mai hawa 3 ya ruguje a kasuwar GSM titin Beirut, yana mai cewa, “Da farko wannan wuri ya kamata ya zama wurin ajiye motoci kawai, ya yi kankanta da aikin shaguna. A cikin farin ciki da 'yan kasuwar suka yi, a ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, ya tunatar da cewa, an kafa wani kwamitin kwararru mai karfi da zai binciki musabbabin aukuwar lamarin. "Ya kamata mu sani cewa, daga farko duk wani gini ya kamata a tsara shi tare da kulawa da kwararru. A cikin mako guda kawai wannan Kwamitin zai gabatar da rahotonsa. Kuma za mu yi aiki da shi yadda ya kamata," in ji shi.

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su baiwa ma’aikatan da ke aikin ceton hadin kai, inda ya kara da cewa, “Bayan an tono wurin yadda ya kamata, nan take gwamnati za ta fara samar da filin ajiye motoci da ya dace. Gwamna Ganduje yana tare da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da wasu kwamishinoni da wasu manyan jami'an gwamnati.

169 views0 comments
bottom of page