top of page
  • Writer's pictureArtv News

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi wa manyan hafsoshinta garambawul


Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi wa wasu manyan hafsoshi da kwamandojinta sauyin wuraren aiki a abin da ta kira kokarin inganta ayyukanta yayin da kasar take kara fuskantar matsalolin tsaro.


A wata sanarwa da darektan hulda da jama'a na rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ya ce babban hafsan sojojin kasa na Najeriyar Laftana Janar Faruk Yahaya ne ya amince da garambawul din.


Hukumomin sojin sun bayyana wannan mataki ne dai 'yan sa'o'i bayan wata ganawa ta musamman da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da manyan shugabannin tsaro sakamakon matsalar tsaro da take kara tabarbarewa a Najeriyar.


BBC Hausa ta rawaito cewa a yayin taron ne shugabannin sojojin kasar suka sheda wa Buharin cewa sun bullo da wasu sabbin dabaru da za su fuskanci kalubalen tsaron da kasar ke fama da shi a yanzu.


Ko a jiya Alhamis da daddare wasu 'yan bindiga sun kai hari shingen bincike na sojoji da ke kusa da dutsen Zuma, a Madalla ta jihar Naija dab da iyaka da babban birnin tarayya Abuja.


Wasu daga cikin manyan hafsoshin da garambawul din ya shafa sun hada da Manjo Janar UT Musa daga hedikwatar sojoji ta runduna ta 81 zuwa hedikwata ta runduna ta 82 inda aka nada shi a matsayin babban kwamanda (GOC).


Sai Manjo Janar TA Lagbaja daga hedikwatar runduna ta 82 zuwa hedikwatar runduna ta 1, inda yanzu ya zama babban kwamandanta.


Yayin da Manjo Janar AS Chinade aka dauke shi daga depo ta rundunar sojin zuwa hedikwatar sojojin ta runduna ta 2, aka kuma nada shi babban kwamanda.


Wadannan na daga cikin tarin sauye-sauye da rundunar sojin ta kasa ta yi wa manyan hafsoshin a fadin Najeriya.

56 views0 comments
bottom of page