top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ronaldo ba zai bar United ba


Duk da jita-jitar da ake yi cewa Ronaldo zai bar Manchester United zuwa wata kungiyar da za ta buga Champions League, amma alamu na nuna babu ina za shi.


Masu sharhi sun tsinkayi hakan ne tun bayan ganin dan wasan da aka yi zai shiga motar United zuwa wasan da za ta fafata na Premier da Leicester City a ranar Alhamis.


Ko da yake dai dan wasan na benci, kamar sauran wasannin da ya buga a kungiyar na Premier, amma dai ba a ji duriyar cewa zai bar kungiyar ba.


Kuma an jiyo kocin Manchester United Erik ten Hag a wani taron manema labarai yana cewa "babu inda Ronaldo zai je a kwanakin karshe na musayar yan wasa".


Ronaldo dai ya nemi ya bar Old Trafford a farkon wannan kakar domin buga gasar zakarun Turai, kuma an ta alakanta shi da kungiyar Atletico Mardid da ke Spaniya, da Chelsea da Bayern Munich.


Idan Ronaldo ya zauna a kungiyar zai buga gasar Europa kenan, karon farko cikin tarihin rayuwar dan wasan.

(BBC HAUSA)

4 views0 comments
bottom of page