top of page
  • Writer's pictureICT Consult

Rikicin ɗariƙu ya jawo ƙone-ƙone a Dorayi Babba da ke Jihar Kano

Wani rikici mai nasaba da addini a unguwar Dorayi Babba da ke birnin Kano a arewacin Najeriya ya haddasa ƙone-ƙone a yammacin ranar Litinin.




Mazauna unguwar sun shaida wa BBC Hausa cewa rikicin ya samo asali ne tsakanin wani mutum mabiyin Shi'a da maƙotansa sakamakon fili da ya mallaka a unguwar.

A cewarsu, wasu mazauna unguwar ne ke adawa da taron da mabiya Shi'a ɗin kan gudanar a filin nasa kuma suka nemi a daina, abin da ya jawo har aka ƙona motar mutumin.

Rundunar 'yan sandan Kano ta faɗa wa BBC Hausa cewa ta kama mutum huɗu sannan kuma tana ci gaba da bincike kan lamarin.

"Bayan ya ƙi dainawa sai mutanen suka yi tayin sayen filin nasa kan miliyan 12 amma ya ce ba zai sayar ba, suka ce miliyan 15, nan ma ya ce a'a," a cewar mazauna yankin.

"Mutumin ya ce shi sai miliyan 50 zai sayar da filin. Daga baya ya sake tara mutane don ci gaba da taron Shi'a. Shi ne mutane suka fusata suka ƙona motarsa."

0 views0 comments
bottom of page