Kano Pillars ta koma ta uku a teburin Firimiyar Najeriya
Updated: Aug 3, 2021
Kano Pillars ta yi nasarar doke Wikki Tourists da ci 1-0 a wasan mako na 37 a gasar Firimiyar Najeria da suka kara ranar Litinin

Pillars ta ci kwallon ne ta hannun Auwalu Ali Malam daf da za a tashi daga fafatawar da suka yi a jihar Kaduna.
Da wannan sakamakon Pillars ta koma ta uku da maki 64 da tazarar maki daya tsakaninta da Nasarawa United ta biyu a teburin gasar bana.
Da yake saura wasa daya ya rage a kammala karawar shekarar nan, Akwa United ce ke jan ragama da maki 71.
Rivers United ta hudu a teburi da Enyimba ta biyar kowacce tana da maki 63 da tazarar maki daya kenan tsakaninsu da Pillars.
Can a karshen teburi kuwa sun hada da Sunshine Stars ta 17 da maki 42 da Warri Wolves ta 18 maki 41 a mataki na 18 a kasan teburi.
Wadda take ta 19 ita ce FC IfeanyiUbah mai maki 36 sai Adamawa United ta 20 mai maki 25, bayan buga wasanni 37.