Artv News
Rasha na garkuwa da Afrika ne ta hanyar mamaya a Ukraine- Zelensky

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce mamayar da Rasha ta yi wa kasarsa ya sanya nahiyar Afirka a matsayin wacce aka yi garkuwa da ita musamman yadda mamayar ta jawo wa nahiyar karanci abinci
Sai dai Kyiv ta ce ta shiga tattaunawa don samar da dama wajen fito da hatsin da aka tare a tekun Black Sea sakamakon shingen da sojojin ruwan Rasha suka sanya.
Mamayar da Rasha ta yi ya dakatar da jiragen ruwa a tashar jiragen ruwa ta Ukraine fita da hatsin kasar duk da kasancewarta daya daga cikin masu samar da abinci a duniya, lamarin da ke barazanar jefa miliyoyin mutane cikin hadarin yunwa.
Kawo yanzu dai an gaza samar da wata hanyar shawo kan Rasha ta kawo karshen mamayar da ta ke yi a Ukraine.
A cewa shugaba Volodymyr Zelensky yanzu haka ya fara tattaunawa da kasashe da kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Afirka, don lalubo hanyar magance matsalar.