Artv News
Ranar Yaki da Cin Hanci: Matsalar sai karuwa ta ke yi a Afrika - Transparency International

Ranar 9 ga watan Disamba ce ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya. Kungiyoyin da ke fafutuka domin yaƙi da cin hancin a Najeriya sun ce ana ci gaba da samun karuwar matsalar a kasashen Africa.
Auwal Musa Rafsanjani, na kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transperancy International a Najeriya, na da ra'ayin cewar abin takaici ne a ce har yanzu dukkan matakan da kasashen Afirka ke cewa suna dauka kan matsalar amma har yanzu ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Ya ce: "A gaskiya, duk da kokarin da hukumomi suke yi da kuma fafutukar da kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa ke yi, har yanzu akwai matsalar cin hanci da ta yi kanta, ta dada iza wutar rashin tsaro saboda kudaden da ake warewa domin inganta tsaro, amma ake sama da fadi da su."
Ya kara da cewa kudaden da aka ware domin yi wa talakawa aiki a bangaren kiwon lafiya da kuma yadda ake bayar da kwangilolin gine-gine sun zama manyan matsaloli a nahiyar Afirka.
Da aka tambaye shi ko ana samun ci gaba a yaki da cin hanci da rashawa a kasashe kamar
Najeriya, sai Auwal Rafsanjani ya ce:
"Akwai sauran jan aiki a gaba, in dai har ba za a magance yadda ake sayar da kuri'ar zabe, ko raba 'yan takara da jami'yyarsu ta siyasa, babu yadda za a ce ana yaki da cin hanci, domin ta nan ne ake shigowa ana tatse dukiyar kasa."
A kan matakan da suka dace a dauka domin kawar da abubuwan da ke tarnaki ga yaki da cin hanci da rashawa, Auwal Rafsanjani ya ce tilas shugabanni su zama adilai, masu gaskiya da bin doka. Ya kuma ce ya kamata su bayyana kaddarorinsu tun ma kafin a zabe su.
"Bayan sun sauka kuma ya dace a duba a ga abin da suka mallaka."
Cikin abubuwan da ake bukata kuma akwai kauce wa takura wa 'yan jarida da masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa da wasu hukumomin ke yi.
Ya kuma ce da shugabannin Najeriya za su bude kunnuwansu su ji shawarwarin da ake ba su domin a kyautata yaki da cin hanci da rashawa, kuma a tabbata an toshe hanyoyin da ake bi wajen sace arzikin kasa, da abubuwan sun inganta, maimakon yadda ake mayar da yakin batu na siyasa.
BBC