Artv News
Pogba na dab da komawa Juventus

Paul Pogba na dab da komawa Juventus bayan da kwantiransa ya kare a Manchester United a kakar da ta wuce.
Ana sa ran za a gwada koshin lafiyar dan wasan tawagar Faransa, mai shekara 28 a karshen mako, daga nan ya sa hannu kan kwantaragin.
BBC ta rawaito cewa Pogba ya koma United daga Juventus a 2016 kan fam miliyan 89 a matakin wanda aka saya mafi tsada a tamaula a duniya.
United ta kasa kulla yarjejeniya da Pogba, domin ya ci gaba da taka leda a Old Trafford, daga nan ta sanar cikin watan Yuni cewar dan wasan tawagar Faransa zai bar kungiyar.
Ana sa ran Pogba zai fara karbar horo a Juventus a mako mai zuwa a lokacin da take shirin zuwa Amurka domin buga atisayen tunkarar kakar bana.
Juventus za ta buga wasan sada zumunta a Amurka da Barcelona ranar 27, sannan kwana uku tsakani ta fafata da Real Madrid.
Kaka biyu a jere, Juventus tana yin ta hudu a teburin gasar Serie A da tazarar maki 16 tsakaninda da AC Milan, wadda ta dauki kofin kakar da ta wuce.
Juventus ta ci karo da koma baya, bayan da ta lashe Serie A karo tara a jere, inda Pogba ya bayar da gudunmuwa a daukar kofin da ta yi tsakanin 2012-13 zuwa 2015-16.
Ya ci kwallo 34 a wasa 178 a Juventus, wadda ya koma taka leda a 2012, bayan da kwantiraginsa ya kare a Old Trafford a matasan kungiyar.
A kakar farko a Old Trafford, Pogba ya dauki League Cup da Europa League daga nan kuma ya fara fuskantar kalubale.