top of page
  • Writer's pictureArtv News

Paris St-Germain ta nada Luis Campos a matsayin daraktan kwallon kafa


Kungiyar kwallon kafar Paris St-Germain ta nada Luis Campos a matsayin daraktan kwallon kafa.


A baya dan kasar ta Portugal ya rike mukamin daraktan wasanni a Monaco da Lille.


Ayyukan da ya yi a kan musayar 'yan kwallon kafa sun taimaka wa Lille wajen lashe gasar Ligue 1 a kakar 2020-21, lokacin da suka yi nasara a kan PSG, ko da yake ya bar kungiyar a watan Disamba na 2020.


"Ina matukar farin cikin zuwa Paris St-Germain. Ina kallon su a matsayin kungiya da ke da manyan burika da kwazo a duniya tamaula," a cewar Campos, mai shekara 57.

"Muna da manufa iri daya, manufar da na yarda da ita, kuma na zaku na soma aiki domin kawo ci gaba ga kungiya."


Campos na zuwa kungiyar ne a daidai lokacin da aka samu sauyi mai girma a Parc des Princes, inda daraktan kwallon kafa Leonardo ya bar su sannan ake sa ran kocinsu Mauricio Pochettino zai bar kungiyar a bazara.


Majiyarmu ta ce PSG ta sake lashe kofin Lig na Faransa a kakar wasan da ta wuce, sai dai ta sha kashi a hannun Real Madrid a wasan 'yan-16 na Gasar Zakarun Turai.

2 views0 comments
bottom of page