Artv News
NDLEA ta kama tsohon -soja ɗan shekara 90 da laifin kai wa ƴan ta’adda ƙwayoyi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA ta kama wani ɗan shekara 90, Usman Adamu a Mailalle, Sabon Birni a Sokoto da laifin kai wa ƴan fashin daji ƙwayoyi.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya faɗi hakan a wata sanrwa da ya fitar jiya Lahadi a Abuja.
Babafemi ya ce an kama wanda a ke zargin ne tun 3 ga watan Agusta.
Ya ƙara da cewa an kama shi ne da kilo 5.1 na tabar wiwi.