Artv News
Nassir Ali Ahmed ya sake cin zaben fitar da gwani a karo na hudu
Daukacin wakilai 55 da suka kada kuri’u a zaben da aka yi na fitar da gwani a karamar hukumar Nassarawa,sun sake zabar Nassir Ali Ahmed a matsayin wanda zai sake tsayawa APC takarar dan majalisar garayya

. Zaben tabbataccen wanda aka gudanar a ofishin Hisba na karamar hukumar, ranar Juma’a, ya biyo bayan shawarar da aka yi na bai-daya ta hanyar amincewar juna a gidan gwamnatin Kano tsakanin Nasiru Ali Ahmad da Lamin Sani. Lamin Sani wanda shi ma dan takara ne, da Nasiru Ali Ahmad, an ce ya amince cewa babu wata hujja da za ta kalubalanci shi biyo bayan nasarorin da ya samu a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya daga karamar hukumar. Wakilinmu ya bamu rahoton cewa yin hakan sun share wa Gwamnatin Ganduje da kuma shugabannin Zartarwar Jam’iyyar na Jiha damar barin Nasiru Ali Ahmad ya tafi neman kujerarsa ba tare da wata hamayya ba. Sai dai kuma domin tabbatar da zaben, an baiwa wakilai damar kada kuri’unsu wanda Jamilu Sani Rano mai sa ido na jam’iyyar APC a jihar ya jagoranta, jami’an INEC, DSS, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro. An kirga kuri'un inda Nasiru Ali Ahmad ya samu kuri'u 55 ya lashe dukkan kuri'un da aka kada. Da yake jawabi, Nasiru Ali Ahmad, ya godewa Allah da ya yi ishara da nasara, inda ya ce, shi ke ba da mulki ga wanda yake so, ya kara da cewa babu wata gaba tsakaninsa da Lamin Sani, domin ‘yan uwan juna ne. Ya kuma bada tabbacin cewa bayan ya ci zabe zai ci gaba a inda ya tsaya domin yiwa mazabar sa Kano da Najeriya alfahari.