top of page
  • Writer's pictureArtv News

Najeriya ta tafka asarar sama da Dala biliyan guda da rabi a badakalar Malabu


Gwamnatin Najeriya ta tafka asarar kudin da ya kai sama da Dala biliyan guda da rabi a shari’ar da take yi da Bankin JP Morgan dangane da safarar kudin cinikin rijiyar danyan man fetur mai lamba OPL 245 wanda ake dangantashi da badakalar Malabu. Mai shari’a Sara Cockerill dake kotun Birtaniya ta yanke wannan hukunci yau, saboda abin da ta kira gazawar gwamnatin Najeriya na gamsar da ita cewar an damfare ta wajen cinikin rijiyar man.

Najeriya ta shigar da karar ce inda ta bukaci a biya ta sama da Dala biliyan guda da miliyan 700 saboda rawar da Bankin JP Morgan ya taka wajen baiwa kamfanin Shell da Eni damar zuba kudaden cinikin rijiyar man a asusun tsohon ministan man kasar Dan Etete.

Lauyan Najeriya Roger Masefield, a watan Fabarairu ya bayyana cewar abinda ake bukata daga wurin ta shine shaidar almundahana da kuma tabbatar da cewar bankin JP Morgan na da masaniya akai.

Lauyan ya ce bisa hakkin gudanar da ayyukan banki, JP Morgan na da hurumin kin biyan kudaden da ake magana akai muddin ya tabbatar da cewar ana shirin damfarar abokin huldar sa ne. Mai shari’a Cockerill ta ce lokacin da aka biya kudaden a shekarar 2013, Bankin yana da labarin hadarin dake tattare da biyan kudaden amma kuma takaitacce ne.

A shekarar 2011 kamfanin Shell da Eni sun biya gwamnatin Goodluck Jonathan ta wancan lokaci Dala biliyan guda da miliyan 300 domin mallakar rijiyar man, yayin da daga cikin kudin suka biya kamfanin mai da iskar gas na Malabu mallakar tsohon ministan mai Dan Etete Dala miliyan 875.

Wannan ya biyo bayan matakin da Etete ya dauka na mikawa kamfanin Malabu rijiyar man lokacin da yake rike da mukamin ministan mai a shekarar 1998.

Makwanni bayan kulla yarjejeniyar a watan Afrilun shekarar 2011, aka kwashe rabin kudaden da aka biya kamfanin Malabu, aka rarraba wa manyan jami’an gwamnatin Najeriya da kuma shugabannin kamfanonin man kasashen Yammacin duniya a matsayin cin hanci.

Wannan ya sa gwamnatin Najeriya ta kaddamar da bincike domin gano wadanda suke da hannu cikin badakalar da kuma neman ganin an karbo kudaden daga hannun su, amma sai wata kotu a Milan ta wanke shugabannin kamfanonin man da ake zargi da amfana da kudaden.

Jaridar Premium Times ta ruwaito gwamnatin Najeriya ta bayyana bacin ranta da hukuncin wanda ta ce za ta yi nazari akai domin sanin matakin da za ta dauka nan gaba. A nashi bangare Bankin JP Morgan ya ce hukuncin ya tabbatar da matsayinsa na gudanar da ayyukansa bisa ka’idar doka, kuma ko yaushe a shirye yake domin kare kimarsa.



10 views0 comments
bottom of page