Artv News
Najeriya ta kai matakin dab da na kusa da karshe a gasar mata ta Kofin Duniya

Tawagar kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekara 20 ta kai matakin dab da na kusa da karshe a gasar kofin duniya a Costa Rica, bayan da ta ci Koriya ta Kudu 1-0.
To sai dai Ghana ba za ta kai zagayen gaba ba a wasannin, bayan da ta kara shan kashi a wasa na biyu a rukuni na hudu.
Wasan na rukuni na uku da Falconets ta buga an samu tsaikon awa daya kafin a fara, bayan da guguwa da iska da zubar ruwan sama ya mamaye filin wasa na Alejandro Morera Soto.
Tun kan hutu Koriya ta Kudu ta yi ta kai hare-hare ga ragar Nageriya, amma haka suka je hutu ba ci.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Falconets ta kara kwazo, inda saura minti bakwai a tashi daga karawar Esther Onyenezide ta ci kwallo.
Falconets wadda ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Jamus a gasar 2010 da kuma 2014 ta fara da cin Faransa 1-0 a wasan farko a rukuni na uku.
Ranar Alhamis Najeriya za ta fuskanci Canada a wasa na uku kuma na karshe a rukunin da Canada, wadda ta sha kashi a wasa biyu da ta kara.
Ghana daya daga cikin mai wakiltar Afirka ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Japan a wasa na biyu a rukuni na hudu.
Ghana wadda ba ta haura wasannin cikin rukuni a karo na biyar da take halartar wasannin kofin duniya, za ta buga da Nertherlands ranar Alhamis.
Najeriya
(BBC HAUSA)