top of page
  • Writer's pictureArtv News

Mutane 155 sun mutu sakamakon girgizar kasa a Afghanistan



Akalla mutane 155 suka rasa rayukansu, yayin da sama da 200 suka samu rauni sakamakon wata girgizar kasa mai karfin gaske da ta auku a Afghanistan a cikin daren da ya gabata. Ana fargabar adadin mamatan ya karu ganin irin girmar barnar da ibtila’in ya haifar a yankin Paktika da ke kusa da iyakar Pakistan.

Ma’aikatar Tunkarar Aukuwar Bala’o’i ta Afghanistan ta ce, an samu mafi asarar rayukan ne a Lardin na Paktika, inda anan kawai mutne 100 suka mutu.

RIF ta ce,Wasu hotuna da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda girgizar kasar ta yi rugu-rugu da gidajen al’umma.

Girgizar kasar dai na dauke da karfin maki 6.1 kamar yadda masana daga Amurka suka bayyana.

13 views0 comments
bottom of page