top of page

An maye gurbin mukamin Abba Kyari da Tu

Updated: Aug 3, 2021

Babban sufeton janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya amince da naɗin DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT)Wannan na nufin shi zai maye gurbin ɗan sanda nan Abba Kyari da aka dakatar kan zargin rashawa.

Sanarwar da ke dauke da sa hannun jami'in yaɗa labaran rundunar, CP Frank Mba ta ce DCP Disu zai kama aiki gadan-gadan ba tare da ɓata lokaci ba.

Kuma a cewar sanarwar IGP Alkali na saran sabon shugaban ya nuna ƙwarewa da jagoranci wajen aikawatar da aikinsa da sauke nauyin da aka dora masa.

Sannan ya tabbatarwa ƴan kasa cewa wannan sashi na IRT zai ci gaba da aiki tuƙuru wajen kare kasa da manufofinta daga ɓata gari.

Kafin naɗin DCP Disu wannan mukamin, shi ne tsohon kwamandan kai agajin gaggawa na Rapid Response Squad (RRS) ta jihar Legas. Kuma ya rike mukamin mataimakin kwamshina a sashin ayyuka na rundunar a hedikwatarta ta Abuja.

Sannan ya rike mukamai daban-daban da ayyuka a fanoni da dama na rundunar.

4 views0 comments
bottom of page