top of page
  • Writer's pictureArtv News

Masu garkuwa da mutane sun saki tsofaffin Shugabannin NFF a NajeriyaRundunar yan sandan Najeriya ta sanar da cewa masu garkuwa da mutane sun saki tsofaffin Shugabannin Hukumar Kwallon kafa ta kasar NFF.

Majiyarmu ta ce, tun da farko masu garkuwar sun bukaci kudin fansar mutanen, da suka hada da tsohon Sakatare Janar da NFF din Sani Ahmed Toro.

An kuma yi garkuwa da su ne karshen makon da ya wuce, tare da tsohon kocin yan wasan Najeriya yan kasa da shekara 23 Garba Ila da Isah Ja, a kan haryarsu ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Sai dai babu bayanai kan ko an biya kudin fansa ne kafin sakin mutanen.

Sani Toro ya shafe shekara shida yana jan ragamar NFF daga 1993 zuwa 1999.

Najeriya na fuskantar matsalar rashin tsaro da ya hada da garkuwa da mutane don neman kudin fansa musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar.

5 views0 comments
bottom of page