top of page
  • Writer's pictureArtv News

Manchester United ta kammala daukar Antony daga Ajax kan £82m


Manchester United ta kammala daukar dan wasan Brazil Antony daga Ajax kan yuro miliyan 95 kwatankwacin fan miliyan 82.


Cinikin, wanda za a cikin yuro miliyan 5 na wasu tsarabe-tsarabe shi ne na hudu mafi tsada a tarihin Premier.


Dan wasan mai shekara 22 ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar zuwa 2027, da kuma zabin karin shekara guda.


"Wannan ba karamin lokaci ba ne mai tarihi a rayuwata, na shiga kungiyar da take daya daga cikin mafiya shafara a duniya" in ji Antony.


"Ina godiya ga kowa, musamman wadanda suka dora yardarsu a kaina, musamman iyalaina, da masu horas da ni da abokan wasana, saboda da babu su da ban zo inda nake ba a yau.


Buga kwallo a karkashin Erik Ten Hag ba karamin abu ba ne a wurina."


Antony ya ci kwallo 24 ya kuma bayar da 22 an ci, cikin wasa 82 da ya buga a Ajax.

A 2020 ne ya koma Ajax daga Sao Paulo karkashin koyarwar Erik Ten Hag.


Ya ci wa Ajax kwallo 11 a Champions ya kuma ci wa Brazil biyu a wasa tara tun a watan oktobar 2021 da ya fara bugawa kasar tasa.


Dan wasan shi ne na biyar da Manchseter United ta saya a wannan kakar biyo bayan Lisandro Martinez, da Casemiro da Tyrell Malacia da kuma Christian Eriksen.


United ta kashe sama da fan miliyan 210 a wannan kakar karkashin Ten Hag, kuma ta sallami yan wasa da dama da suka hada da Pogba da Jesse Lingard da Juan Mata, sai kuma Nemanja Matic da Edinson Cavani da kuma Andreas Pereira.


(BBC HAUSA)

8 views0 comments
bottom of page