top of page
  • Writer's pictureArtv News

Manchester United ta doke Crystal Palace da ci 3-1


Manchester United ta casa Crystal Palace da ci 3-1 a wasan sada zumunta a shirin tunkarar kakar bana da suka kara a Amurka ranar Talata.


United ta fara cin kwallo ta hannun Anthony Martial, bayan da sabon dan wasa Tyrell Malacia ya bai wa Diogo Dalot tamaula ta bangaren hagu, shi kuma ya buga wa Martial, wanda ya sa kirji ya kuma buga da kafa ta fada raga.


Haka aka kammala minti 45, United da kwallo daya a raga ita kuwa Palace na nema.

Minti uku da suka koma fafatawar zagaye na biyu ne United ta kara na biyu ta hannun Marcus Rashford, wanda Donny van de Beek ya bashi tamaula.


Kungiyar Old Trafford ta kara na uku, bayan da Rashford ya bai wa Martial tamaula, shi kuma ya tura wa Jadon Sancho, wanda bai bata lokaci ba ya zura a raga.


Minti na 74 Palace ta zare daya ta hannun Joel Ward, haka ta wuce David de Gea ya kasa tare kwallon, wanda a baya ya hana Ademola Ola-Adebomi zura masa kwallo a raga.


To sai dai United ta kammala wasan sada zumunta da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Will Fish jan kati.


Karo na biyu United na yin nasara a wasan sada zumunta a Amurka a bana, bayan da ta doke Liverpool 4-0 tun farko.

6 views0 comments
bottom of page