top of page
  • Writer's pictureArtv News

Man United ta amince Ronaldo ya bar kungiyar a kakar nan


Watakila Manchester United za ta bar Cristiano Ronaldo ya bar Old Trafford a lokacin da ake cinikayyar 'yan kwallo a kakar nan.


United ta damu kan rashin karsashin dan kwallon tawagar Portugal da hakan ke shafar kwazon kungiyar.


Tun can baya sabon kociyan United, Erik ten Hag ya sanar cewar Ronaldo mai shekara 37, bana sayarwa bane.


Wasu masu sharhin wasanni sun ce United tana da karsashi ta kuma taka rawar gani a wasannin sada zumunta da ta yi a Thailand da Australia kan fara kakar nan.


Ronaldo yana da saura kwantiragin kaka daya a Old Trafford, amma yana neman kungiyar da za ta buga Champions League a bana.


United ta kammala a mataki na shida a kakar da ta wuce, kenan za ta kara a Europa League a kakar nan.


Rashin nasara a wasa biyu a jere da United ta yi a Premier League a hannun Brighton da Brentford ya nuna karara yadda Ronaldo ke dana sanin sake komawa Old Trafford daga Juventus.


United wadda ta kasa cin wasa biyu tana ta karshe a kasan teburin Premier League, za kuma ta karbi bakuncin Liverpool ranar Litinin 22 ga watan Agusta.


Wanda ya lashe Ballon d'Or biyar shi ne kan gaba a ci wa United kwallaye a bara kuma na uku a cin kwallaye a Premier, bayan Mohamed Salah da Son Min.


Chelsea ta sanar da hakura da zawarcin Ronaldo a watan jiya, wanda aka yi ta alakanta shi da zai koma Bayern Munich da kuma Atletico Madrid.

13 views0 comments
bottom of page