top of page
  • Artv News

Man City ta kammala daukar Gomez daga Anderlecht


Manchester City ta tabbatar da kammala daukar matashin dan kwallon tawagar Sifaniya ta 'yan shekara 21, Sergio Gomez daga Anderlecht.


Mai shekara 21 zai koma taka leda a Etihad kan yarjejeniyar kaka hudu kan fam miliyan 13 da karin fam miliyan 11 kudin tsarabe-tsarabe.


Gomez ya fara tamaula a makarantar matasan Barcelona daga nan ya koma taka leda karkashin tsohon kyaftin din City, Vincent Kompany a kungiyar Belgium.


Gomez zai saka riga mai lamba 21 a City, wadda dan kasar Sifaniya David Silva ya yi amfani da ita.


Silva ya dauki Premier League hudu da wasu karin kofi 10 a lokacin da ya taka leda a Etihad.

City ta dauki mai tsaron bayan ne, sakamakon da Brighton ta sayar da Marc Cucurella ga Chelsea, wanda ta taya aka ki sallama mata.


Kungiyar Etihad ta dauki Gomez domin ya maye gurbin Oleksandr Zinchenko, wanda Arsenal ta saya a bana..


Bayan da dan kwallon Ukraine ya koma Gunners, yanzu Joao Cancelo ne kadai fitatce a gurbin, sai wani matashi Josh Wilson-Esbrand.


Koci Pep Guardiola ya fada a baya cewar da kyar ne idan zai bayar da aron Gomez ga wata kungiyar.

(BBC HAUSA)

3 views0 comments
bottom of page